Isa ga babban shafi
Amurka-Kenya

Shugaba Obama na Amurka ya isa Kenya

Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama ya isa kasar Kenya a yammacin yau, inda ya fara ziyarar aiki na kwanaki biyu kuma a karon farko kenan da Obama ya ziyarci kasar wadda ta kasance tushen mahaifinsa tun bayan darewarsa kan karagar shugabancin Amurka. 

Shugaba Barack obama na Amurka ya fara ziyar aiki a kasar Kenya
Shugaba Barack obama na Amurka ya fara ziyar aiki a kasar Kenya REUTERS/Jonathan Ernst TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

A cikin jirgin sama samfarin Airforce One shugaban na Amurka ya isa filin tashi da saukan jaragen sama na kasa da kasa dake birnin Nairobi babban birnin Kenya.

Jim kadan da saukarsa shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya yi hannu da Obama tare da rungumeshi yayin da ake sa ran cewa a ziyar ta kwanaki biyu, Obama zai gabatar da jawabi a taron zuba hannayen jari da za a gudanar kuma zai tattauna da hukumomi a kan sha’anin tsaro da ayyukan ta’adanci harma da batutuwan da suka shafi Demokradiyya da ‘yancin bil-adama.

Dubban jama’ar Kenya ne dai suka yi dandazo a hanyar wucewar jerin Motocin da Obaman ke ciki da kuma za su wuce dashi zuwa masaukinsa yayin da jirgi mai saukan ungulu ke ta shawagi a sama.

An dai karkafa matakan tsaro a birnin Nairobi, inda aka rufe wadansu sassa na birnin tare da hana jiragen sama tashi da sauka saboda ziyarar shugaban wanda daga nan zai wuce kasar Habasha ranar lahadi mai zuwa.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.