Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha-Syria

Taron kasashen duniya kan rikcin Syria a birnin Vienna

A yau juma’a ministocin harkokin wajen kasashen Rasha, Saudiyya, Turkiyya da kuma Amurka, na gudanar da taro a birnin Vienna na kasar Austria, taron da ake fatan zai share fage a kokarin da ake na kawo karshen rikicin Syria.

Ministocin harkokin wajen Rasha, Amurka, Saudiyya da kuma Turkiyya a taron Vienna kan rikcin Syria
Ministocin harkokin wajen Rasha, Amurka, Saudiyya da kuma Turkiyya a taron Vienna kan rikcin Syria REUTERS/Carlo Allegri
Talla

Ministan harkokin wajen Rasha kasar da ke mara wa Bashar Assad baya Sergei Lavrov da takwaransa na Amurka John Kerry, na ganawa da ministocin harkokin wajen kasashen Turkiyya da kuma Saudiyya, wadanda dukkaninsu ke mara wa ‘yan tawaye baya a rikici na Syria.

Kasashen Amurka, Turkiyya da kuma Saudiyya, na kokarin ganin sun shawo kan kasar Rasha ne, domin tilasta wa Bashar Assad sauka daga karagar mulki ta hanyar kafa gwamnatin rikon kwarya wacce ba zai taka rawa a cikin ta ba.

To sai dai lura da irin rawar da Rashan ke takawa tun daga ranar 30 ga watan satumbar da ya gabata a yakin da ake gwabzawa a Syria da kuma ziyarar da shugaba Assad ya kai a birnin Moscow cikin wannan mako, hakan ya sa manazarta na ganin cewa abu ne mai wuya taron na yau ya iya samar da mafita ga rikicin.

A daya bangare kuwa kasashen Rasha da Jordan, ta bakunan ministocinsu na waje, sun bayyana a birnin na Vienna cewa, za su yi aikin soja a tare a cikin kasar ta Syria.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.