Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha-Syria

Amurka da Rasha na tattaunawa kan hare-hare su a Syria

Amurka na zaman tattaunawa da Rasha kan hare-haren da suke kai wa Syria gudun karo da juna a Sararrin Samaniya, zaman da ke zuwa bayan Rasha ta kaddamar da sabbin hare-hare 40 kan moboyar ISIS da ke Syria a kasa da Sa’o’i 24.

Jiragen Rasha dake kaddamar da hari a Syria
Jiragen Rasha dake kaddamar da hari a Syria REUTERS
Talla

Sakataren Ma’aikatar tsaron Amurka Ashton Carter ya ce tattaunawarsu na yau zai mayar da hankali ne kan hanyoyin kawar da matsala a hare-haren da bangarorin 2 ke kaiwa kan mayakan ISIS a Syria

Carter ya ce duk da dai suna bayyana shakunsu kan Rasha, ganawar ya zama tilas domin gudun karo da juna.

Tattaunawar Amurka da Rasha na zuwa ne, bayan rahotanni a yanzu na bayyana tasirin da harin Rasha ke yi kan ISIS sama da wanda Amurka da kaweyanta ke kaiwa kasar sama da shekara 1.

Ko a yau sai dai gwamnatin Moscow ta sanar da kaddamar da sabbin hare-hare 40 a yankin Aleppo, Idlib, Latakia da Dier Ezzor kan mayakan.

Sai dai har yanzu Amurka na jadada cewa harin Rasha ba yana zuwa kan ‘yan ta’ada ba ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.