Isa ga babban shafi
EU-RASHA

EU ta bukaci Rasha da ta dakatar da kai hare hare a Syria

Kungiyar Tarrayar Turai ta EU a yau litinin ta bukaci kasar Rasha da ta gaggauta dakatar da hare haren da take kaiwa a kasar Syria.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin Reuters/路透社
Talla

Shugabar harkokin wajen kungiyar Federica Moghereni ta kira hare haren Rasha a Syria a wani abu da ya kara wargaza yunkurin samar da zaman lafiya tare da jefa rayuwar al’umma cikin kuncin, Moghereni ta kara da cewa hare haren Rasha zasu kara haifar da Karin yan ta’ada tare da zafafa rikicin da aka kwashi tsawon lokaci ana yi.

Yayin da kungiyar Eu ta yi kira da babban murya na kawo karshen hare haren Rasha a Syria ganin matakin da Rasha ta dauka ba zai iya magance matsalolin da yaki ya haifar a kasar ba.

A nata bangaren kuwa Rasha ta ce tana kai hare haren ne da niyyar murkushe kungiyar ISIL tare da kawo daidaito da kuma yanayin da za’a iya cimma zaman lafiya inda shugaban kasar Vladimir Putin ya kare matakin Rasha da cewa hare haren ta akan mayakan ISIL ne kawai, kungiyar da Ya ce ke barazana ga zaman lafiyar al’ummar kasar.

A ranar alkhamis mai zuwa ne shugabanin kungiyar ta EU zasu yi taro kuma batun rikicin kasar Syria da ya lakume rayuka sama da dubu dari biyu tare da tilasata kusan rabin al’ummar kasar tserewa daga gidajensu shi zai kasance batun da taron zai fi mayar da hankali akai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.