Isa ga babban shafi
Amurka

Clinton : Amurka ba za ta iya hana faruwar ta’addanci ba a duniya

Tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta bayyanawa majalisar dokokin kasar cewa, ba ta yadda Amurka za ta hana faruwar ayyukan ta’addanci a duniya, kuma kasar za ta ci gaba da kasance a cikin hatsarin yiwuwar kai ma ta hari.

Hillary Clinton ta Jam'iyyar Democrat na Amurka
Hillary Clinton ta Jam'iyyar Democrat na Amurka REUTERS/Scott Morgan
Talla

Hillary Clinton ta gurfana a gaban majalisar ne domin amsa tambayoyi dangane da kisan da ‘yan ta’adda suka yi wa jakadan Amurka a birnin Benghazi da ke gabashin kasar Libya kimanin shekaru 3 da suka gabata Christopher Stevens, a matsayinta na sakatariyar harkokin wajen kasar a wancan lokaci.

Cliton ta ce ba ta yadda Amurka za ta iya hana faruwar hare-haren ta’addanci, ko tabbatar da tsaro a ko’ina, to amma dole ne kasar ta kasance a cikin hatsarin fuskantar irin wadannan hare-hare.

A lokacin da ‘yan ta’adda suka kai wa ofishin jakadancin na Amurka da ke Benghazi hari, ko baya ga jakadan Christoper Stevens, akwai wasu Amurkawa uku da suka rasa rayukansu dukkaninsu ma’aikatan diflomasiyya.

To sai dai shekaru uku bayan faruwar lamarin, Amurkawa da dama ne ke ganin cewa an yi sakaci sosai wajen bai wa jami’an diflomasiyyar kasar kariya musamman a kasashen da Amurka ke gudanar da ayyukan fada da ta’addanci cikinsu kuwa har da Libya, dalilin haka ne kwamitin musamman da majalisar ta kafa domin duba wannan batu ya gayyaci Hillary Clinton domin samun bahasi daga gare ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.