Isa ga babban shafi
Girka-Bakin Haure

MDD na furgaban makomar Bakin Haure Sakamakon hunturu

Majalisar Dinkin Duniya ta sake bayyana damuwarta kan kwararan bakin haure a Turai, lura da yadda ake tunkarar lokacin hunturu, yayin da kasashen Turai ke daukan matakan rufe iyakokinsu.

Bakin haure da ke cigaba da neman Mafaka a Turai
Bakin haure da ke cigaba da neman Mafaka a Turai REUTERS/Ognen Teofilovski
Talla

‘Yan sanda Girka sun shaidawa Kamfanin Dilancin labaran Faransa AFP cewa a jiya litinin Bakin haure dubu 8 ne suka isa Girka, duk da garadi da ake yi na rashin kyawun yanayi, kuma a kullum karuwa suke.

A shekarun baya lokutan hunturu, a kan samun raguwar bakin da ke ketara tekun Meditettanean zuwa Turai, amma a wannan karon abubuwa sun sha ban-ban, domin a wuni guda ana samun adadin baki dubu 9 da ke tsallaka tekun.

Mai Magana a madadin hukumar ‘yan gudun hijira ta duniya Joel Millman ya ce masu aikin safaran bakin na nuna rashin damursu kan hatsarin da ke tatare da yin haka a wannan yanayi, dalilan da ya sa suke son cimma matsaya da Turkiya domin shawo kan matsalar.

A kwananki 9 da suka wuce bakin haure 19 ne suka rasa rayukansu yayin tsallaka Turkiya zuwa Girka

A yanzu dai bakin haure 3,135 ne suka mutu a tekun daga farko shekarar zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.