Isa ga babban shafi

Turai ta fara magance masu safarar bakin haure

An fara gudanar da wani aikin Soji na musamman domin kama masu safarar bakin haure a tekun Mediterranean, inda aka tanadi jiragen ruwa na yaki mallakar kasashen Turai domin sintiri a tekun da nufin cafke masu safarar bakin.

Dubban 'Yan gudun hijira ne ke bi ta tekun Mediterranean domin shiga kasashen Turai.
Dubban 'Yan gudun hijira ne ke bi ta tekun Mediterranean domin shiga kasashen Turai. REUTERS/Yannis Behrakis
Talla

A watan da ya gabata ne Shugabar harkokin wajen Kungiyar Tarayyar Turai, Federica Mogherini ta bayyana cewa an shirya wani aikin Sojin ruwa mai taken EUNAVFOR MED domin magance masu safarar dake haifar da hasarar rayukan bakin haure sakamakon hadarin jiragen ruwa dake ritsa wa da su a tekun.

Tuni dai aka girke jiragen ruwa na yaki 6 a gabar ruwan Libya da aka bayyana a matsayin babbar hanyar da masu safarar suka fi amfani da ita wajan safarar bakin hauren zuwa Turai.

Har ila yau an tanadi jirgin ruwan Italiya mai daukan jirgin sama, da jirgin ruwan yaki na Faransa harma da na Birtaniya da Spain, sai kuma jiragen ruwa biyu mallakar kasar Jamus.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.