Saudiya na bincike kan al’amarin da ya auku a masallacin Makkah
Gwamnan birnin Makkah na Saudiya Yarima Khaled al-Fisal ya bada umarni gudanar da bincike kan ruftawar karafan fadada gini a Masallacin ka’aba a jiya Juma’a wanda ya yi ajali Mahajatta akalla 107.
Wallafawa ranar:
A cewar hukumomin tsaron kasar yanzu haka akwai mutane kusan 238 da suka samu munanar raunin ka, kuma akwai yiyuwar samun karuwan adadin mamatan.
Wannan lamari ya kasance mumunar bala’i da ta auku kan Mahajjata tun bayan shekarar 2006 da daruruwan mahajatta suka rasa rayukansu sakamakon turmutsu-tsu.
Kawo yanzu dai ba a Fitar da bayanai kan ‘yan kasar da hatsarin ya rutsa da su ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu