Isa ga babban shafi
Saudi-Arabia

Sama da Alhazai 80 sun rasu a Masallacin Ka'aba dake Makka

Akalla mutane 87 sun rasa rayukansu sakamakon ruftawar wadansu karafan daga kayayyakin gine- gine a cikin Masallacin Ka’aba dake Kasar Saudiya kamar yadda hukumomin Kasar suka sanar a yau jumma’a.

Masallacin Ka'aba dake Makka a Kasar Saudiya
Masallacin Ka'aba dake Makka a Kasar Saudiya REUTERS/Muhammad Hamed
Talla

Hukmomin sun kara da cewa kimanin mutane 184 sun jikkata sakamakonhadarin wanda ya auku a dai dai lokacin da ake aikin fadada ginin Masallacin na Ka’aba.

Wannan kuma na zuwa ne a yayin da dubban musulmai daga sassa dabam dabam na duniya suka ziyarci Kasar domin sauke aikin Hajji da aka saba gudanar duk shekara.

Hotunan da aka yi ta yadawa ta shafukan sada zumunta sun nuna mutane kwance jina- jina a harabar Masallacin kuma tuni aka tura jami’an bada agajin gaggawa domin taimakawa.

Tuni dai mahukantan Kasar suka bada umarnin gudanar da bincike kan aukuwar lamarin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.