Isa ga babban shafi
Saudi-Arabia

a karo na Farko kasar Saudi-Arabia ta baiwa matan kasar yanci yin zabe.

A yau lahadi kasar Saudiya ta shiga sabon babi irinsa na farko a tarhi bayan da amince da takarar diya Mata a zaben kananan hukumomin da ake shirin gudanarwa a watan December wannan shekara ta 2015 a kasar, matakin da masu hankoron neman sauyi ke cewa, bai wadata ba a matsayin yanci , a yayin da su kuma masu tsatsauran ra’ayi ke sukarsa.

was Mata a kasar Saudiya
was Mata a kasar Saudiya DR
Talla

Wannan dai shine karo na farko da mata a kasar ta Saudiya, za su kada kuri’a a zaben da za’a gudanar a tarihin kasar

A masarautar ta Saudiya dai, har yanzu batun raba mata da maza tare da rufe kai da kafafu na nan daram kamar yadda musulunci ya tanada

Har ila yau mata a kasar ta Saudiya, basa da ‘yancin yin aikin gwamnati, ko yin Balaguro, tare da Samun Pasport tafiye tafiye, sai da izinin Namiji, ko dai mahaihinta ko kuma mijinta, bugu da kari kuma haramun ne su tuka mota ko wani abin hawa a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.