Isa ga babban shafi
Saudi-Arabia

Sama da Mutane 100 sun rasu a Masallacin Ka'aba na Makka

Akalla mutane 107 sun rasa rayukansu yayin da 238 suka jikkata sakamakon rubtawar wasu karafan daga kayyakin gine-gine cikin Masallacin Ka’abah dake Makka a Saudiya kamar yadda hukumomin Kasar suka sanar.

An danganta aukuwar lamarin sakamakon ruwa da aka yi kamar da lbakin kwarya mai hade da iska mai karfi
An danganta aukuwar lamarin sakamakon ruwa da aka yi kamar da lbakin kwarya mai hade da iska mai karfi REUTERS/Ali Al Qarni
Talla

Mai Magana da yawun Masallantan Ka’aba da Madina, Ahmad bin Muhammad Al-mansoori ya bayyana cewa hadarin ya faru ne a jiya Jumma’a da misalin karfe 5 na yamma agogon Kasar sakamakon ruwa da akayi kamar da bakin kwarya kuma mai hade da iska mai karfin gaske.

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da al-umman Musulmai daga sassan duniya suka ziyarci Kasar da nufin yin aikin Hajji kamar yadda aka saba gudanarwa duk shekara.

Hotunan da aka yi ta yadawa ta shafukan sada zumunta sun nuna mutane kwance jina- jina a harabar Masallacin kuma tuni aka tura jami’an bada agajin gaggawa domin taimakawa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.