Isa ga babban shafi
Amurka

An Kashe wani jigon Kungiyar Khorasan ta Syria

Hukumomin Kasar Amurka sun bayyana cewa an kashe Bafaranshen nan da ake zargi da kera wa Mayakan Kungiyar Khorasan mai alaka da Al-Qaeda Bama bamai.

A baya dai an zaci Bafaranshen ya mutu
A baya dai an zaci Bafaranshen ya mutu AFP PHOTO / MOHAMMED HUWAIS
Talla

A jiya jumma’a ne Hukumomin suka sanar da mutuwar David Drugeon sakamakon hare haren saman da Rundunar hadin gwiwa ta kai a Syria.

A baya dai Amurka ta zaci an Kashe Drugeon tun a watan Nuwamban bara amma daga bisani ta fahimci yana raye.

To sai dai a wannan karan hatta mayakan jihadi na Saudiya sun sanar da mutuwar Bafaranshen a shafin sada zumunta na Twitter, inda suka ce ya yi shahada.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.