Isa ga babban shafi
Yemen-Saudiya

Al-Qaeda ta kai hari a ofishin 'yan sandan kasar Yemen

Mayakan al-Qaeda sun kai hari a shalikwatar Sojin kasar Yemen dake kula da Hadramawt da wani bangare na Shabwa inda suka ruguza gini mai hawa uku, lamari dake zuwa kwana guda bayan tarwatsa offishin ‘yan sanda Mukalla dake kasar.

Wasu mayakan al-Qaeda
Wasu mayakan al-Qaeda
Talla

Mayakan na al-Qaeda sun yi amfani da bama-bamai wajen tarwatsa ginin Ofishin, da kuma baza ya’yan kungiyar a kewayean Mukalla, bayan samun bayanai dake cewa kasashen dake kawance, karkashin jagoranci Saudiya za su taimakawa dakarun gwamnatin kasa ta Yemen, wejen fara kai musu hare-hare.

Tun cikin watan Maris, Saudiya da kawayenta suka kaddamar da hari kan mayakan Huthi mabiya shi‘a, ba tare da tankawa rikicin al-Qaeda ba.

A ranar Talata da ta gabata ne dai rahotanni ke cewa dakarun saudiya 100 sun isa birnin Aden, kuma za su taimaka wajen kare yankunan da al-Qaeda ke neman mamayewa.

Yayin da ake tunanin kura ta fara lafawa a wasu yankunan kasar Yemen, musamman birnin Aden bayan kwace ikon birnin daga hannun mayakan Huthi, yanzu haka rikcin na al-Qaeda ne ke kokarin zama barazana, domin a ‘yan kwanankin nan an zarge su da harin kan ofishin ‘yan sandan birnin Aden, da kuma hari kan ofishin hukumar leken asiri dama asibitin sojojin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.