Ban Ki-moon yace Al Qaeda ce ta kai hare hare a Syria
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon yace Kungiyar Al-Qaeda ce ta kai wasu munanan hare haren bom a birnin Damascus a kasar Syria, wanda ya yi sanadiyar mutawar mutane da dama.
Wallafawa ranar:
“Kwanaki da suka gabata, akwai harin bama bamai a Syria, kuma na yi imanin kungiyar al Qaeda ce ta kai hare haren. Wannan wata matsala ce da ta kunno kai.” Inji Ban Ki-moon a lokacin da yake ganawa da matasa a Hedikwatar Majalisar a Birnin New York.
Ban Ki-moon yace adadin wadanda suka mutu a Syria yanzu sun haura 10,000 tun fara zanga-zangar adawa da gwamnatin Bashar Al Assad.
Mista Ban yace Shugaba Bashar al-Assad ya ki fara aiwatar da shirin zaman lafiya ta Kofi Annan mai shiga tsakanin rikicin kasar.
A ranar 10 ga watan Mayu ne wasu ‘Yan kunar bakin wake suka tayar da bama bamai a birnin Damascus, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 55 da raunata kusan 400.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu