Dakarun UAE sun ceto dan Ingilan da Al-Qaeda ta kama
Jami’an tsaron Haddadiyar Daular Larabawa, sun ceto wani dan asalin Kasar Ingila da Kungiyar Al-Qaeda ta yi garkuwa da shi sama da watanni 18 a Kasar Yemen.
Wallafawa ranar:
A watan Fabairun da ya gabata ne Al-Qaeda ta kama Douglas Robert Semple mai shekaru 64 kuma ma’aikacin Man Fetur, a lokacin da yake aiki a lardin Hadramwat, inda mayakan jihadi ke da karfi.
Rahotanni sun ce an yi nasarar ceto Semple ne a wani samame da jami’an suka kai kuma tuni suka kai shi birnin Aden, inda daga nan ya tafi Abu Dhabi a cikin Jirgin sama.
Dakarun haddadiyar daular larabawa na cikin rundunar da Saudiya ke jagoranta domin yaki da mayakan Houthi a Yemen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu