Isa ga babban shafi
Amurka-Yemen

Amurka ta bayyana damuwa ga hare haren da Saudiya ta kai Yemen

Kasar Amurka ta bayyana damuwarta akan hare haren jiragen Sama da Saudiya da kawayenta suka kai a garin Hodeida a Yemen wanda ya lalata tashar ruwan da ake shigar da kayan jin kai ga al’ummar kasar da ke cikin mawuyacin hali.

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama Reuters/路透社
Talla

Saudiya da kawayenta sun kai harin ne kan mayakan Huthi ‘yan Shi’a a ranar 18 ga watan Agusta ‘amma rahotanni sun ce ma’aikata da dama ne suka mutu a tashar ruwan Hodeida.

Tashar ruwan dai hanya ce da ake shigar da kayan jin kai da suka hada da abinci da magani da ruwan fetir zuwa ga mutanen Yemen.

Bayanai sun ce kusan kashi 80 na mutanen Yemen na cikin mawuyacin hali, yayin da sama da miliyan suka fice kasar saboda yakin da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da ‘Yan tawayen Huthi da kuma luguden wuta da jiragen yakin Saudiya da kawayenta ke yi a Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.