Isa ga babban shafi
Yemen

Amnesty ta bukaci bincike a game da zargin aikata laifufukan yaki a Yemen

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta bukaci kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya gudanar da bincike a game da zargin aikata laifufukan yaki a Yemen, wanda daga watan Maris mutane dubu hudu da dari uku suka rasa rayukansu.

Talla

A rahoton da ta fitar a yau, kungiyar ta ce dakarun kawance a karkashin jagorancin Saudiyya, sun kashe fararen hula masu tarin yawa a hare-haren da suke kai wa kasar ta sama, kuma ba sa bambantawa tsakanin ‘yan tawaye da fararen hula a duk lokacin da suke kai hari, saboda haka akwai bukata Majalisar Dinkin Duniya ta binciki lamarin.

Rikicin kasar dai ya kazance ne bayan mayakan Houthis sun yi kokarin kwace mulki daga hannun shugaba Abdourabuh Mansour Hadi, al’amarin da ya tilastawa shugaban tserewa tare da samun mafaka a kasar Saudiya.

A rahoton da hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta fitar tace rikicin ya hallaka mutane 4,345 a cikin kasar kuma yawancin su farraren hula ne.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.