Isa ga babban shafi
Yemen

Dakarun Gwamnatin Yemen na samun nasara a Aden

Sojojin gwamnati sun yi nasarar kwato fadar gwamnati da ta fada hannun mayakan hutti a tsawon watanni hudu da aka kwashe ana rikici a kasar, a yayin da aka soma gudanar da ayyukan sufuri a filin jirgin sama bayan saukar wani jirgin Soja a birnin na Aden.

Jirgi ya fara sauka a filin saukar jirage a Aden na Yemen
Jirgi ya fara sauka a filin saukar jirage a Aden na Yemen REUTERS/Stringer
Talla

Jim kadan da isar dakarun gwamnatin da suka samu horo na musanman tare da rakiyar dakarun kasar Saudiya a kasar suka kwace birnin Aden daga hannun mayakan na huthi.

‘Yan tawaye 30 ne suka mutu a musayar wutar da aka yi tsakanin bangarorin biyu a kokarin karbe fadar gwamnati.

Kazalika jirgin yakin kasar Saudiya yau ya sauka a filin jirgin saman kasar ta Eden a karo na farko dauke da kayan agaji bayan sake karbe filin jirgin daga ikon mayakan Huthi.

Ministan Sufurin Yemen Badr Basalma ya ce akwai injiniyoyi da za su isa kasar domin gudanar da ayyukan gyare gyare a filin jirgin, tare da cewa za a ci gaba da gudanar da ayyukan da suka kun shi karbar kayyakin agaji domin kai dauki ga al’ummar kasar da rikicin kasar ya daidaita.

Yanzu haka dai sojin kasar Yemen sun sami horo tare da karin makamai na zamani da ya ba su damar karya lagon mayakan huthi ‘Yan Shi ‘a.

Majalisar Dinkin Duniya tace acikin l’ummar kasar Yemen sama da miliyan 21 kashi 80 na bukatar taimako na kayan abinci da sauran kayan more rayuwa

Tun watan Maris da ya gabata ne kasar Saudiya tare da gungun kawanyenta ma kasashen larabawa, suka kaddamar da yaki domin hana ‘yan tawayen Huthi karbe madafan ikon Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.