Isa ga babban shafi
Yemen

Jirgin Sojin Saudiya ya sauka a birnin Aden na Yemen

A karon farko bayan kwace ikon tashar jirgin sama da ke Aden na kasar Yemen, Jirgin sojin kasar saudiya ya sauka a fillin jirgin wanda aka shafe tsahon watanin 4 a rufe sakamakon rikicin kasar.

Tashar jirgin Sama na birnin Aden dake Yemen
Tashar jirgin Sama na birnin Aden dake Yemen REUTERS/Stringer
Talla

Tuni dai ma’aikatar sufurin kasar ta sanar cewa an fara amfani da tashar jirgin, da dakarun kawance karkashin jagoranci saudiya suka kwato daga hannu mayakan Huthi a makon daya gabata.

Kuma ana saran cikin ‘yan kwanakin nan a fara jigilar kayayyakin jin kai zuwa kasar domin taimakawa fararran hula.

Dakarun dake goyon bayan Shugaban Kasar ne Abdur-Rabuh Mansur Hadi suka yi nasarar kwato filin tashi da saukan jirgin saman na birnin Aden bayan sun fatattaki mayakan Huthi.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.