Isa ga babban shafi
Amurka-Iran

Obama ya samu amincewar Majalissar dattawa kan shirin Nukiliyar Iran

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya samu gagarumin rinjayen Majalissar dattawan kasar kan shirin Nukiliyar Iran, batun da ke kara nuna gamsuwar shirin a duniya.

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama Reuters/路透社
Talla

A baya dai ‘yan majalisar dokokin Amurka da dama basa goyon baya wannan shiri, lamari da aka yi tunanin zai ta’azara takunkumai tattalin arziki a Tehran da kuma haifar da nakasu a fadada shirin Nukiliyar ta.

Yayin da ‘yan Republican da dama ke gargadin cewar da wuya shirin nukiliyar Iran ya kasance na zaman lafiya.

A wannan lokacin dai Barbara Mikulski wacce ta jima a majalisar dattijan kasar na Jam’iyyar Democrat ce ta fara nuna goyon bayan ta ga wannan shiri, inda a yanzu haka ake da yawan ‘yan majalissar dattawa 34 da ke marawa Obama ba ya kan shirin Nukuliyar.

A cewar Mikulski wannan mataki kawai ne zai bada zaman lafiya da hana Iran yin wani yunkuri samar da makaman Nukiliyar cutar wa, sai dai kuma ta ce duk da sun amince za su kuma tabbatar cewar ba a cutar da Isra’ila ba.

Su dai ana su bangaran ‘yan republican da ke adawa da wannan shirin basu da cikakken hadin kai, sai dai kuma suna gargadi cewa sassautawa Iran takunkumai zai taimaka mata wajen samun kudin da yawan su ya kai dala biliyan 150 wanda kuma za ta iya amfani da su wajen taimakwa kungiyoyin ta’addanci a duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.