Isa ga babban shafi
Amurka-Isra'ila

Isra’ila ce kawai ke adawa da yarjejeniyar Iran- Obama

Shugaba Barack Obama ya kare matakin da Amurka da sauran manyan kasashen duniya suka dauka, na kulla yarjejeniyar Nukiliya da Iran. Shugaban ya ce Isra’ila ce kawaia ta fito fili tana adawa da yarjejeniyar da suka cimma bayan shafe lokaci mai tsawo suna tattaunawa da Iran.

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama REUTERS/Jonathan Ernst

Talla

Shugaba Obama, da ke jawabi a jami’ar birnin Washington, ya gargadi ‘yan majalisar dokokin kasar, da cewa kin amincewa da sasanta rikici ta turbar Diplomasiyya, zai iya haifar da yaki.

Dandalin da Obama ke jawabi, nan ne wajen da tsohon shugaba Kenedy ya bukaci a nemi zaman lafiya da tsohuwar tarayyar Soviet cikin shekarar 1963, lokacin da ake fargabar amfani da makamin Nukiliya.

Shugaban ya yi kira ga ‘yan majalisar dokokin kasar, da kar su mika wuya ga masu kokarin ci gaba da kushe yarjejeniyar da aka kulla da Iran, inda ya ce duniya ta riga ta fahimci abin da ya dace.

Cikin shekarar 1979 Mahukunta Washington suka raba gari da Tehram, bayan juyin juya halin da sanadiyyarsa aka yi garkuwa da ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka su 52, tsawon kwanakin 444.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.