Isa ga babban shafi
Iran

Khamenei ya ce babu tabbas kan makomar yarjejeniyar Nukiliyar Iran

Jagoran juyin-juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyed Ali Khamene’i ya ce babu tabbas a game da makomar yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kasar da sauran kasashen duniya dangane da shirin nukiliyyar kasar.

Ayotollah Ali Khamenei Jagoran juyin-Juya halin Musulunci Iran
Ayotollah Ali Khamenei Jagoran juyin-Juya halin Musulunci Iran
Talla

Khamenei wanda shi ne ke da karfin zartas da hukuncin karshe dangane da wannan yarjejeniya a cikin Iran, ya bayyana cewa Amurka ta yi ruwa da tsaki domin samar da yarjejeniyar ne saboda ta samu damar shiga a cikin Iran.

To sai dai ya ce a Amurka ko kuma a Iran, ba wanda ya ke da tabbacin cewa za a aiwatar da wannan yarjejeniyar da aka sanya wa hannu ranar 14 ga watan yulin da ya gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.