Isa ga babban shafi
Tunisia

Birtaniya ta bukaci ‘yan kasarta su fice Tunisia

Biritaniya ta shawarci ‘yan kasarta da ke zaune a kasar Tunisia da su tattara su bar kasar, domin akwai alamun ana iya sake kai masu munanan hare hare a cikin kowane lokaci.

'Yan sandan Tunisia a wajen Shakatawa
'Yan sandan Tunisia a wajen Shakatawa REUTERS/Zohra Bensemra
Talla

Wannan gargadi na zuwa ne makwanni biyu bayan kazamin harin da aka kai kan masu yawon shakatawa yawancinsu Turawan Birtaniya a bakin ruwan Tunisia, inda aka kashe mutane 38.

Ana ganin Wannan mataki zai shafi tattalin arzikin kasar Tunisia wadda ta ke takama da samun makudan kudade daga ‘yan kasar Turai da ke zuwa yawon shakatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.