Isa ga babban shafi
Tunisiya

Gwamnatin Tunisia ta kori Gwamnan Jihar Sousse da 'Yan Sanda da yawa saboda sakaci

Shugaban kasar Tunisia ya yi waje rod da wasu manyan jami'an Gwamnati da dama ciki akwai Gwamnan jihar Sousse, sakamakon mummunar hari na jihadi makon jiya da ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan kasashen waje 38. 

Harabar da aka yi kisan a wurin hutawa na gaban teku dake Sousse na Kasar Tunisia
Harabar da aka yi kisan a wurin hutawa na gaban teku dake Sousse na Kasar Tunisia REUTERS/Zohra Bensemra
Talla

Mashawarcin Fira Ministan kasar gameda sadarwa Dhafer Neji ya sanar da Koran.

‘Ya Sanda da yawa aka sallama daga aikin nasu saboda sakaci wajen aiki.

Shugaban kasar Tunisia Beji Caid Essebsi , yau asabar ya bayyana kafa dokar ta baci bayan kisan masu yawon shakatawa da akayi a gaban ruwan kasar cikin makon jiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.