Tunisia
Faransa, Jamus da Britaniya za su taimakawa Tunisia wajen yaki da Ta’addanci
Kasashen Faransa, Jamus da Birtaniya sun bayyana goyan bayan su ga gwamnatin kasar Tunisia kan yaki da ta’addanci lokacin da ministocin kasar suka kai ziyarra kwana guda inda aka kai harin da ya hallaka baki 'yan kasashen waje 38.
Wallafawa ranar:
Talla
Sakatariyar harkokin cikin gidan Birtaniya wanda ta rasa mutane mafi yawa a harin, Theresa May ta ce babu yadda za’ayi yan ta’adda su samu nasara kan al’umma.
Tunisia ta ce an gano mutane 25 da aka kashe, cikin su harda 'yan kasahsen Ireland, Jamus, Belguim, Portugal da Russia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu