Isa ga babban shafi
Yemen-alQaeda

Kungiyar al-Qaeda ta ce an Kashe ma ta wani Jagora a Yemen

Kungiyar Al-Qaeda ta gaskata mutuwar Nasir al-Wuhayshi daya daga cikin na sahun gaba cikin manyan kwamadojin ta a kasar Yemen, sakamakon harin da wani jirgi da babu kowa ciki, na kasar Amurka ya kai masa.

Nasur al-Wuhayshi mataimakin Shugaban kungiyar al Qaeda da aka kashe
Nasur al-Wuhayshi mataimakin Shugaban kungiyar al Qaeda da aka kashe ©REUTERS/Reuters TV
Talla

Bayanai dai na nuna cewa tun mutuwar madugun kungiyar ta al Qaeda Osama Bin Laden ba'a sami wani babban da kungiyar al Qaeda ta rasa ba kamar shi Nasur al-Wuhayshi.

Kungiyar ta tabbatar da mutuwarsa ta wani hoton video data fitar, inda ta bakin kakakinta Khalid Omar Batarfi, ta ce shi da wasu mujahidai biyu akayi hasara.

Gwamnatin Amurka tun chan baya ta yi tayin kudin Amurka Dolla miliyan 10 ga duk wanda ya kyankyasa mata inda yake ko kuma ya aika dashi lahira.

Nasur al-Wuhayshi ya kasance na hannun daman Osama Bin Laden ne sosai domin yana cikin wadanda suka karbi horo na musamman a kasar Afghanistan

Bayanai na cewa a shekara ta 2002 ya tsere daga Afghanistan yayi Iran inda aka kama shi aka dankawa Yemen. Kuma a shekara ta 2006 hake rami ya yi tare da wasu 22 ya sulale daga gidan yari da ake tsare dashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.