Isa ga babban shafi
Yemen

‘Yan tawayen Yemen sun fice fadar gwamnati a Aden

‘Yan tawayen kasar Yemen sun fice daga birnin Aden fadar shugaban kasar Abderabbo Mansur Hadi bayan jiragen yakin Saudiya sun yi ma su luguden wuta a daren Alhamis. ‘Yan tawayen sun kwace ikon garin Aden ne a kudancin Yemen bayan sun gwabza fada da dakarun da ke biyayya ga shugaba Hadi.

Dakarun da ke biyayya ga Shugaban Yemen Abd Rabbo Mansour Hadi a Aden
Dakarun da ke biyayya ga Shugaban Yemen Abd Rabbo Mansour Hadi a Aden REUTERS/Anees Mansour
Talla

Wani Jami’in gwamnati a Aden ya ce ‘Yan tawayen na Huthi mabiya Shi’a sun fice fadar Hadi da safiyar Juma’a. amma wasu rahotanni sun ce mayakan sun fake a yankin Khor Maksar kusa da fadar gwamnatin a Aden.

Wannan na zuwa ne bayan da kasar ta shiga rudani sakamakon sakin da mayakan Al-Qaeda suka yi wa wasu fursunoni, lokacin da suka balle wani gidan yarin kasar.

Rahotanni sun ce Mayakan Al Qaeda sun karbe ikon Mukalla babbar birnin lardin Hadramawt da ke kudu masu gabacin Yemen a yau Juma’a inda suka kubutar da fursononi da dama.

Rikicin Yemen dai ya rikide tsakanin mabiya Shi’a da Sunni, inda al Qaeda ta bayyana kaddamar da Jihadi akan mabiya Shi’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.