Isa ga babban shafi
Yemen

Mayakan Al Qaeda sun balle gidan yarin Yemen

Mayakan kungiyar Al Qaeda sun abka wa wani gidan yari da ke kudu maso gabacin kasar Yemen a yau Alhamis tare da sakin fursunoni 300 ciki har da shugaban kungiyar Khalid Batarfi wanda ake tsare da shi tsawon shekaru hudu.

Mayakan Huthi da ke fada gwamnatin Yemen
Mayakan Huthi da ke fada gwamnatin Yemen REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Jami’an tsaro a Yemen sun ce sama da fursunoni 300 suka tsere bayan mayakan al Qaeda sun abka wa gidan yarin da ke lardin Hadramaut.

Kamfanin dillacin labaran Faransa ya ruwaito ce an kashe dogarawan da ke tsaron gidan yarin guda biyu da wasu fursononi guda biyar sakamakon musayar wuta tsakanin Jami’an tsaro da mayakan Al Qaeda.

Rikici a Yemen na ci gaba da kazancewa tun bayan da Mayakan Huthi suka karbe ikon gwamnati.

Mayakan al Qaeda sun yi amfani da rikicin da ake a Yemen na fasa gidan yarin.

Hukumar ‘Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu haka mutanen da ke tserewa daga kasar Yemen suna isa kasar Somalia ta hanyar kwale kwale, sabanin yadda ‘yan Somalia ke tserewa a baya zuwa Yemen.

Hukumar ta ce yanzu haka mutane 32 suka isa Somalia kuma suna fatar ganin wasu sun kara zuwa ganin yadda rikicin Yemen ke kara kamari.

Ratar kilomita 30 ne dai tsakanin gabar ruwan Djibouti da Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.