Isa ga babban shafi
Najeriya

Tarayyar Afrika da Turai sun taya Buhari Murna

Kungiyar Kasashen Afirka AU da Tarayyar Turai sun aike da sakon taya murna ga sabon zababben shugaban Najeriya Janar Muhammadu Buhari, tare da yaba wa shugaba Goodluck Jonathan kan dattakon da ya nuna.

Sabon Shugaban Najeriya Janar Muhammadu Buhari
Sabon Shugaban Najeriya Janar Muhammadu Buhari REUTERS
Talla

Shugabar gudanarwar kungiyar Tarayyar Afrika Nkosazana Dlamini ta ce demokradiyar Najeriya ta kara daukaka.

Babbar jami’ar diflomasiyar kasashen Federica Mogherini ta ce tana fatar aiki tare da Janar Buhari a lokacin mulkinsa.

Mogherini ta kuma yaba wa shugaba Goodluck Jonathan mai barin gado saboda rawar da ya taka wajen gina kasar da kuma dattakun da ya nuna wajen amincewa da sakamakon zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.