Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ne sabon Shugaban Najeriya

Janar Muhammadu Buhari na Jam’iyyar adawa ta APC ya lashe zaben Najeriya da rinjayen kuri’u sama da miliyan biyu, kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar. Buhari ya doke shugaba mai ci Goodluck Jonathan na PDP wanda shi ne karon farko a tarihin siyasar Najeriya da Jam’iyyar adawa ta doke Jam’iyya mai ci.

Magoya bayan Janar Muhammadu Buhari
Magoya bayan Janar Muhammadu Buhari AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Nasarar Buhari dai wani sabon babin dimokuradiya aka bude a Najeriya bayan kawo karshen mulki Jam’iyyar PDP da ta shafe shekaru 16 tana mulki tun 1999 da aka kawo karshen mulkin Soja.

Dubban magoya bayan Janar Buhari ne suka bazama saman titi suna murna a sassan Najeriya tun a daren jiya kafin a bayyana sakamakon zaben a hukumance.

Hukumar Zaben Najeriya tace Buhari ya lashe zaben ne da Kuri’u miliyan 15,424,921 daga cikin kuri’un da aka kada miliyan 28,587,564.

01:30

RAHOTO: Hukumar zabe ta tabbatar da Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

Jonathan na Jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 12,853,162.

Goodluck Jonathan ya amsa shan kaye tare da taya Buhari murna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.