Isa ga babban shafi
Zaben Najeriya

Sabbin fuskoki a Majalisar Dattijan Najeriya

Sakamakon zaben ‘Yan Majalisun da ke ci gaba da fitowa na nuna cewar za a samu sabbin fuskoki a Majalisar Dattawan kasar, cikin su har da Gwamnonin da ke kare wa’adinsu, inda kuma wasu daga cikinsu suka sha kaye a zaben.

Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso
Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso pointblanknews.
Talla

Cikin Gwamnonin da suka kasa samun nasarar zaben zuwa Majalisar Dattawan sun hada da Gwamnonin Jam'iyyar PDP a Jihohin Niger da Kebbi da Bauchi, kamar yadda tsoffin ‘Yan Majalisu irinsu Abdul Ningi da Ahmed Makarfi da Ahmed Aruwa suka kasa samun nasara.

Sabbin fuskoki a Majalisar Dattijan sun hada Gwamnonin da suka samu nasara Rabiu Musa Kwankwaso na Kano da Aliyu Wamakko na Sokoto da Godswill Akpabio na Akwa Ibom da Jonah Jang na Filato da Theodore Orji na Abia.

Akwai Janar Jerry Useni daga Filato da Kwamred Shehu Sani daga Kaduna da Dino Melaye daga Kogi da Abdullahi Abubakar Ojo daga Jigawa.

Wasu daga cikin wadanda suka samu damar komawa Majalisar sun hada da Mohammed Nazif Gamawa da Adamu Aliero.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.