Isa ga babban shafi
Mexico

Shugaban Mexico ya amince a binciki dukiyar shi

Shugaban kasar Mexico Enrique Pena Nieto ya sanar da bayar da umarnin a binciki manyan gidajen da ya mallaka da na matarsa da Ministan kudin kasar, domin sanin ko daga hannun ‘yan kwangila ya same su.

Shugaban kasar Mexico Pena Nieto
Shugaban kasar Mexico Pena Nieto REUTERS/Tomas Bravo
Talla

Shugaban wanda ya ke fuskantar matsin lamba daga mutan kasar game da gidajen kasaita da ya mallaka, ya musanta rashin gaskiya wajen mallakan gine-ginen da ya ke da su.

Ita kanta matarsa kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa ta saye wasu gine-gine na kece raini a Mexico, da ake ganin ba da guminta ta sami kudin ba.

Ana dai zargin Shugaban kasar da matarsa da Ministan kudi sun karbi toshiyar baki daga hannun wasu kamfanin kasar China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.