Isa ga babban shafi
Mexico

Mahaukaciyar guguwa ta yi mummunan ta'adi a kasar Mexico

Wata mahaukaciyar guguwa da kwararru suka sanya wa suna Barbara, ta isa a gabar ruwan kudancin kasar Mexico, kuma kawo yanzu ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 2, cikinsu har da wani tsoho dan shekaru 61 a duniya. Guguwar, wadda ke tare da ruwan sama mai karfin gaske, tana yi tafiyar akalla kilomita129 a kowace sa’a daya, kuma tuni ta haddasa mummunar barna ga gonaki da kuma gidaje har ma da wuraren da ke kunshe da muhimman kayayyaki na tarihi a cikin kasar ta Mexico.Hukumar hasashen yanayi ta kasar Amurka, ta bayyana guguwar a matsayin wadda za ta iya yin illa mai yawa, duk da cewa kawo yanzu ba ta da tabbas idan har za ta shafi wasu yankuna na kasar ta Amurka.  

Wani ta'adi da guguwa ta yi a baya
Wani ta'adi da guguwa ta yi a baya REUTERS/Rick Wilking
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.