Isa ga babban shafi
Faransa-Mexico

An saki Cassez daga gidan yarin Mexico bayan yanke mata hukuncin daurin shekaru 60

An saki Florence Cassez, mai shekaru 38 daga gidan yarin Mexico bayan Kotun kolin kasar tace ‘Yan sandan kasar Sun ci zarafinta a lokacin da suke kokarin cafke ta akan zargin garkuwa da mutane da ya sa aka yanke mata hukuncin daurin shekaru 60 a gidan yari.

Florence Cassez a lokacin da 'Yan Sanda suka kaddamar da harin cafke ta
Florence Cassez a lokacin da 'Yan Sanda suka kaddamar da harin cafke ta 2012 Liberez Florence Cassez.com
Talla

Florence Cassez ta shafe shekaru Bakwai a gidan yari kafin Shugaban kotun Jorge Mario Pardo Rebolledo, ya bayar da umunin sakinta.

Tun bayan da ‘yan sandan kasar suka kama ta, a watan Disambar shekarar 2005, Cassez ta ke musanta zargin da ake mata, na aiki da wani gungun mutane masu satar jama’a, da ake kira Zodiacs da tsohon saurayinta mai suna Israel Vallarta ke jagoranta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.