Isa ga babban shafi
Amurka

Ana ci gaba da ayyukan ceto sakamakon guguwar da ta afka wa Amurka

A kasar Amurka mahaukaciyar guguwar da afka wa jihar Oklahoma, ta yi haddasa mummunar barna ga gidaje da kuma kadarorin jama'a, yayin da makarantu da sauran wuraren kasuwacin suka yi matukar lalacewa. Har ila yau guguwar ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 24 sabanin 91 da aka sanar tun da farko.

Mahaukaciyar guguwar da auku a Oklahoma dake kasar Amurka
Mahaukaciyar guguwar da auku a Oklahoma dake kasar Amurka /www.google.fr
Talla

Rahotanni sun ce kimanin mutane 120 ne cikinsu har da yara kanana ke kwance a gadajen asibiti sakamakon raunin da suka samu sanadiyyar guguwar.

“Mun samu matsananciyar guguwa, wacce ta ratsa cikin unguwanninmu.” Inji Gwamnan Oklahoma, Governor Mary Fallin.

Kafofin yada labaran Amurka sun ruwaito cewa masu ayyukan ceto na ciro yara kanana daga cikin yankin da lamarin ya shafa, yayin da wasu iyaye ke dafifin jiran a kammala ayyukan na ceto.

Tuni Shugaban Barack Obama ya bayyana wajen da lamarin ya auku a matsayin yanki da bala’i ya shafa, ya kuma umurci masu ba da agajin gaggawa da su dukufa wajen kai dauki ga wadanda lamarin ya rutsa da su.

Jihar Oklahoma ta kasance Jihar da ta wuce har zuwa Kudancin Dakota a tsakiyar Jihar Texas, yankin da matsanancin guguwa ke yawan addaba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.