Isa ga babban shafi
Amurka

Shugaban kasar Bama na gudanar da ziyarar aiki a kasar Amurka.

A yau litanin shugaban kasar Amurka Barack Obama na ganawa a fadarsa ta With House da takwaransa na kasar Bama Thein Sein.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama.
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama.
Talla

Ganawar da ta zama ta tarihi domin ita ce ta farko da wani shugaban kasar Bama ya yi da na Amutka, tun bayan wadda aka yi tsakanin shugaba Ne Win na Bama da Lyndon Johnson na Amurka a 1966.

A tsawon shekaru dai, kasar ta Amurka ta kakabawa kasar ta Bama takunkumai domin tilasta wa hukumomin mulkin sojan kasar mika mulki a hannun zababbiyar gwamnatin dimokuradiyya.

A cikin kwanakin da suka gabata ne dai aka gudanar da zabuka a kasar, lamarin da ya sa Amurka ta cire wani bangare na takunkuman da ta kakaba wa kasar, sannan kuma ta gayyaci shugaba Thein Sein zuwa birnin Washington.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.