Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta bayyana sunan sabon Jakadanta a Pakista-Afghanistan

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry, ya bayyana sunan wani kwarre kan harkar Diplomasiyya a kasar ta Amurka James Dobbins, ya kasance Jakadan kasar Amurka a kasashen na Pakistan da Afghanistan.

Afganistan-NATO
Afganistan-NATO REUTERS/Yves Herman
Talla

Wanda aka zaba wato Dobbins ya yi aiki a wurare da dama masu wuyar sha’ani da suka hada da yankin Kosovo, kuma a shekarar 2001 ya daga Tutar kasar Amurkar a birnin Kabul, bayan faduwar gwamnatin Taliban.

Dama dai wannan matsayin na Jakadan kasar Amurka a wadannan kasashen biyu, ya kasance ba kowa a kansa, tun bayan da Marc Grossman ya bayyana ajiye mukamin nasa a cikin Watan Disamba, wanda kuma ya karbi mukamin ne bayan rasuwar Holbrooke a Watan Disamban shewkarar 2010.

Wannan dai wani mataki ne na samar da cigaban wadannan kasashen biyu na Pakistan da Afghanistan da keda alakar Siyasa da ta sha’anin tsaro da kuma tattalin arziki.

An kuma gudanar da wannan nadin ne a yayinda ake saura ‘yan kwanaki kalilan a gudanar da zabe a kasar Pakistan.

Kerry yace ya yita lalaben inda zai samu cancantaccen mutum da za’a sa a wannan mukamin, kuma a halin yanzu ya yi amannar cewar Dobbins zai iya ci gaba da karawa dadaddar dangantakar dake akwai tsakanin Amurka da wadannan kasashen, tare da cimma karshen matsalolin da ake samu a tsakanin su.

Dobbins dai ya taba zama jakadan kasar Amurka a karkashin gwamnatin shugaba Geoge W. Bush, ya kuma taba wakiltar Amurka a wani babban Taro na birnin Bonn daya taimaka aka samar da gwamnati a kasar Afghanistan bayan kwace karfin mulki daga ‘ya’yan kungiyar Taliban.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.