Isa ga babban shafi
India

Tarihi Narendra Modi na Jam'iyyar BJP

Sakamakon zaben da aka gudanar a kasar India ya tabbatar da Narendra Modi na Jam’iyyar BJP a matsayin wanda ya samu nasara da gagarumin rinjaye.To ko wanene Modi ?  

Naredra Modi sabon Firaministan  India
Naredra Modi sabon Firaministan India REUTERS/Amit Dave
Talla

A ranar 17 ga watan Satumban shekarar 1950 ne aka haifi Narendra Modi, a kauyen Mehsana na yankin Vadnagar.

‘Yan asalin gidansu kuma sanannu ne wajen sayar da kayan abinci a kabilar Ganchi-Telli.

Shi ne na uku daga cikin ‘ya’yan mahaifinsu shida da ake kira Damodardas Mulchad Modi da Mahaifiyarsa da aka fi sani da suna Heeraben.

Narendra Modi dai ya taba zaman mai wanke Kofukan Shayi ga mahaifinsa da ke sayar da shayi a Tashar jirgin kasa ta Vadnagar lokacin kurciyarsa.

Ya kuma yi sayar da Shayin tare da yayansa a Tashar Mota, a lokacin yana makaranta a Vadnagar inda Malaman makarantar suka lura yana da hazaka musamman a bangaren muhawara.

Yana saurayinsa ne dai aka yi masa aure da shekara 18 inda ya kuma auri Jashodaben Chimanlal mai shekaru 13 a matsayin matarsa.

Ya shiga harkokin Siyasa a 1971 bayan yakin da aka tafka tsakanin India da Pakistan, yau kuma Modi shi ne sabon shugaban kasa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.