Isa ga babban shafi
India

Za’a saki waɗanda suka kashe Tsohon Firimiyan India daga gidan yari

Gwamnatin ƙasar India ta bayar da umurnin sakin mutane bakwai da aka zarga sun kai harin Bam a 1991 da ya yi sanadin mutuwar tsohon Firaministan kasar Rajiv Gandhi, bayan kotun ƙolin ƙasar ta wanke uku daga cikinsu daga hukuncin ɗaurin rai da rai da aka yanke masu.

Firimiyan India na yanzu Manmohan Singh yana tafiya a kusa da ƙabarin Rajiv Gandhi Tsohon Firaminista
Firimiyan India na yanzu Manmohan Singh yana tafiya a kusa da ƙabarin Rajiv Gandhi Tsohon Firaminista Reuters/
Talla

Mutanen dai sun kwashe tsawon shekaru 23 a gidan yari, kuma kamar yadda rahotanni suka nuna Majalisar ƙasar ta bayar da umurnin sakin mutanen karkashin ikon gwamnati.

Jayalalithaa wanda shi ne babban Minista a Jahar Tamil Nadu yace za’a saki sauran mutanen guda hudu cikinsu har da mace da aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai da rai.

An kashe Gandhi ne a harin ƙunar bakin wake da aka kai Tamil Nadu yankin kudancin India.

Sai dai kuma iyalan tsohon Firaministan sun yi kakkausar suka ga wannan matakin na gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.