Isa ga babban shafi
India

An samu mutuwar Mutane 18 da ke juyayin mutuwar Burhanuddin a India

‘Yan sandan India sun ce akalla mutane 18 suka mutu a birnin Mumbai sakamakon rudani da razana da aka samu a lokacin da daruruwan mutane suka hada gangami domin girmama wani shehin Malamin addinin Islama da ake kira Syedna Mohammed Burhanuddin.

Gangamin Daruruwan 'Yan kabilar Dawoodi sun kewaye motar da ke dauke da gawar Burhanuddin wanda ya mutu yana da shekaru 102 a India.
Gangamin Daruruwan 'Yan kabilar Dawoodi sun kewaye motar da ke dauke da gawar Burhanuddin wanda ya mutu yana da shekaru 102 a India. REUTERS/Danish Siddiqui
Talla

A ranar Juma’a ne Syedna Mohammed Burhanuddin ya rasu yana da shekaru 102 na haihuwa.

Al’amarin ya faru ne a tsakiyar dare bayan an rufe kofar shiga gidan Burhanuddin. Yawan wadanda suka taru ne ya sa mutane suka fara tsorata tare da gudu suna take junansu.

Babban Jami’in ‘Yan sandan Birnin Mumbai, Satyapal Singh yace sama da mutane 40 suka samu rauni.

Burhanuddin, wanda ya rasu kafin ya yi bikin cika shekaru 103 cikin ‘Yan makwanni masu zuwa ya mutu sanadiyar bugun zuciya a gidansa.

Burhanuddin shi ne shugaban kabilar Dawoodi wadanda yawancinsu mabiya akidar Shi’a ne a India.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.