Isa ga babban shafi
India

Kotun India ta tabbatar dokar haramta auren jinsi guda

Kotun kolin kasar India ta tabbatar da tsohuwar dokar haramta aure jinsi guda tun a zamanin mulkin mallaka, inda Yan luwadi da ‘Yan magido za su iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari. Hukuncin na kotun koli ya yi daidai da matakin da babbar kotun birnin Delhi ta dauka na haramta ayyukan luwadi a kasar a shekarar 2009.

Wasu masu fafutikar kare hakkin 'Yan luwadi da madigo suna tafiya a harabar kotun koli a birnin New Delhi na kasar India.
Wasu masu fafutikar kare hakkin 'Yan luwadi da madigo suna tafiya a harabar kotun koli a birnin New Delhi na kasar India. REUTERS/Anindito Mukherjee
Talla

A cikin kundin tsarin mulkin kasar India tun zamanin mulkin mallaka, akwai doka da ke hani da auren jinsi.

‘Yan siyasa da malaman Addini da dama ne suke ta yekuwar ganin kotun kolin kasar ta amince da dokar haramta auren jinsi a kasar. yanzu dai ya rage ga Majalisa ta amince da dokar kamar yadda mai shari’a G.S. Singhvi, yace auren jinsi guda ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar India.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.