Isa ga babban shafi
India

India: Jam’iyya mai mulki ta amsa shan kaye

Jam’iyyar Congress da ta shafe shekaru sama da 10 tana shugabanci a kasar India ta amsa shan kaye a babban zaben kasar da aka gudanar inda alkalumman sakamakon zaben suka bayyana Jam’iyyar Bharatiya Janata mai adawa ta rinjayen kuri’u.

Magoya bayan Jam'iyyar adawa ta BJP a kasar India suna murnar lashe zabe
Magoya bayan Jam'iyyar adawa ta BJP a kasar India suna murnar lashe zabe REUTERS/Danish Siddiqui
Talla

“ Mun amsa Shan kashi” in ji Rajeev Shukla kakakin Jam’iyya mai mulki tare da yin alkawalin ba Jam’iyyar adawa hadin kai.

Tuni magoya bayan Jam’iyyar adawa da Narendra Modi ke jagoranta suka fito saman tituna suna murna.

Sakamakon farko na zaben ya nuna Jam’iyyar adawa ta samu rinjayen kujerun Majalisa 272.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.