Isa ga babban shafi
India

Ana babban zabe a India

Al’ummar kasar India sun fara jefa kuri’unsu a zaben gama-gari na ‘Yan Majalisu da ake gani mafi girma a duniya inda ake fafatawa tsakanin Jam’iyya mai mulki da babbar Jam’iyyar adawa ta BJP da kuma Jam’iyyar AAP mai da’awar yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Jerin gwanon masu kada kuri'a a zaben India
Jerin gwanon masu kada kuri'a a zaben India REUTERS/Rupak De Chowdhuri
Talla

Sama da mutane Miliyan 800 ke da yancin kada kuri’a a zaben wanda Jam’iyyar adawa ta BJP ke fatar kawo karshen mulkin Jam’iyyar Congress da ta shafe shekaru 10 tana mulki a kasar.

Yaki da cin hanci da rashawa da yaki da talauci sune batutuwan da suka mamaye yakin neman zaben Jam’iyyun siyasar da ke takara a zaben na India.

Za’a kwashe zango Tara ana gudanar da zaben har zuwa ranar 12 ga watan Mayu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.