Isa ga babban shafi
Saudiya-Amurka

Obama ya kai ziyara a Saudiya

Shugaban Amurka Barack Obama ya kai ziyara a kasar Saudi Arebiya bayan ya fito daga kasar Italia, kuma Obama zai yi ganawa ta musamman da Sarki Abdallah, domin farfado da amintakar da ke tsakaninsu musamman, sabanin da suka samu akan rikicin Syria da Iran.

Shugaban Amurka Barack Obama yana ganawa da Sarki Abdallah na Saudiya
Shugaban Amurka Barack Obama yana ganawa da Sarki Abdallah na Saudiya REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Akwai ganawa ta musamman da Shugaba Obama na Amurka zai yi da Sarki Abdallah na Saudiya, kuma ziyarar Obama na zuwa ne a lokacin da suke da sabani akan shirin Nukiliyan Iran da kuma rikicin Syria

Tun lokacin da Amurka ke jagorantar manyan kasashen duniya wadanda suka kudiri aniyar sasantawa da Iran akan shirinta na Nukiliya, Saudiya ke adawa da matakin.

Haka kuma Saudiya a baya ta nemi Amurka ta dauki matakin Soji akan Gwamnatin Basharul Assad na Syria game da yin amfani da makamai masu guba akan ‘Yan tawaye.

Saudiya tana ganin idan har aka cim ma yarjejeniya tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, hakan zai iya kara wa Iran karfin fada aji a gabas ta tsakiya musamman kuma Banbancin akida da ke tsakanin Iran mabiya Shi’a da Saudiya mabiya Sunni.

Saudiya dai tana goyon bayan ‘Yan tawayen Syria ne, yayin da kuma Iran ke mara wa Bashar al Assad baya. haka kuma Saudiya ta goyi bayan hambarar Morsi na Jam’iyyar Yan uwa musulmi a Masar. Iran kuma tana mai adawa.

Masana dai suna kallon wannan ziyarar ta Obama a matsayin wani mataki na daidaita sabanin da ke tsakanin Amurka da Saudiya akan rikice rikecn gabas ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.