Kasafin kudi a fannin tsaro zai karu a Duniya-Bincike
A wani rahoton da aka fitar na wata cibiyar da ke bin didigin lamuran tsaro da makamai a duniya IHS ya yi hasashen cewa a karon farko tsawon shekaru biyar, kasafin kudin da ake warewa fannin tsaro zai karu a bana musamman a yankin Asia da Gabas ta tsakiya da kuma Rasha.
Wallafawa ranar:
Rahoton yace adadin kasafin kudin zai karu da sama da kashi daya bayan shafe shekaru adadin na raguwa musamman a kasashen Turai.
Daraktan cibiyar ta IHS yace a tsawon shekaru biyu da suka gabata an samu karuwar kasafin kudin tsaro a kasashen Rasha da China da India da Saudi Arebiya da Oman.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yace zai yi kari ga kasafin kudin da ake kashewa a Fannin tsaro inda tuni adadin da Rasha ke kashewa ya fi adadin da Birtaniya da Japan ke warewa fannin tsaro.
Bakonmu A yau: Dakta Bawa Abdullahi Wase masani Sha'anin tsaro
Kasar Amurka ce dai tafi sauran kasashen Duniya kashe kudi a fannin tsaro kuma adadin yanzu sai raguwa ya ke yi bayan kasar ta fice daga yaki a kasashen Afghanistan da Iraqi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu