Isa ga babban shafi
EU-Masar

Ashton ta gana da Morsi da Sojoji suka hambarar a Masar

Shugabar Ofishin manufofin Ketare na kungiyar Tarayyar Turai Catherine Ashton, ta yi wata ganawa ta tsawon sa’o’I biyu da hambararren shugaban kasar Masar Mohammed Morsi da ke tsare a hannun Jami’an tsaro bayan kifar da gwamnatin shi.

Catherine Ashton, tana ganawa da mataimakin shugaban Masar  Mohamed  el-Baradei kuma babban mai adawa da Morsi
Catherine Ashton, tana ganawa da mataimakin shugaban Masar Mohamed el-Baradei kuma babban mai adawa da Morsi
Talla

Kakakinta Maja Kocijancic tace Ashton ta kwashe tsawon sa’o’I biyu tana ganawa da Morsi game da rikicin siyasar kasar Masar.

Wata majiya tace wani jirgi ne mai saukar Angulu ya dauki Ashton zuwa wajen da ake ci gaba da tsare Morsi cikin tsauraran matakan tsaro.

Tun da farko Ashton ta bukaci a saki Morsi a wata ziyara da ta kawo a ranar 17 ga watan Yuli.

Ashton ta fara ziyarar ne tun a ranar Lahadi kuma ta gana da Shugaban rikon kwarya Adly Mansour da mataimakinsa Mohamed ElBaradei da kuma babban hafsan Sojan kasar Janar Abdel-Fattah al-Sisi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.