Isa ga babban shafi
HRW-Amnesty-Saudiya

Saudiya ta zartar da hukuncin kisa ga mutane 7

Gwamnatin kasar Saudiya ta zartar da hukuncin kisa ga mutane Bakwai da aka kama da laifin yin fashi da makami bayan ta yi watsi da kiran da hukumomin kare hakkin Bil’adama suka yi na kauracewa zartar da hukuncin saboda ya sabawa dokokin kare hakkin Dan Adama na Duniya.

Sarki Abdallah na Saudiya
Sarki Abdallah na Saudiya AFP/Getty Images)
Talla

Wani shedun gani da ido ya shaidawa Kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa an bindge mutanen ne da safiyar Laraba.

Wannan kuma na zuwa ne bayan kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Amnesty ta yi kira ga gwamnatin Saudiya ta dakatar da zartar da hukuncin ga mutanen.

An kama mutanen ne guda bakwai da laifin Fashi da makami wadanda suka abkawa wani shagon sayar da zinari a shekarar 2005.

A shekarar 2009 ne kotun India ta yanke wa mutanen hukuncin kisa da aka bayyana da sunan Sarhan Al Mashaikh da Saeed Al Zahrani da Ali Al Shahri da Nasser Al Qahtani da Saeed Al Shahrani da Abdulaziz Al Amri da kuma Ali Al Qahtani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.