Isa ga babban shafi
India

Mutane 36 sun mutu a taron Kumbh Mela na India

A kalla mutane 36 ne suka mutu, sakamakon turmutsutsun jama’a, yayin da mabiya addinin Hindu ke watsewa daga wuraren ziyararsu, a lokacin bukin addini na Kumbh Mela, a kasar India.

Wasu Indiyawa a wajen taron na Kumbhe Mela a kasar India.
Wasu Indiyawa a wajen taron na Kumbhe Mela a kasar India. REUTERS/Adnan Abidi
Talla

Wasu mutanen da dama sun mutu, lokacin da ake kammala bukin na kwanaki 55, da fiye da mutane miliyon 30 suka halarta a bakin tekun Gages, a Arewacin kasar.
 

Jami’an yankin sun ce makaran gadar da mutane suke tafiya ne suka karye, lamarin da ya yi sanadiyyar hadarin, na taron da ya fi kowanne yawan jama’a aduniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.