Isa ga babban shafi
Pakistan

Pakistan da India sun cimma matsayar tsagaita wuta

Kasashen Pakistan da India sun cimma matsaya ta tsagaita wuta a yanki Kashmir. Wannan matsaya da suka dauka na zuwa ne bayan wata sanarwa da Ministan harakokin wajen kasar Pakistan Hina Rabbani Khar, ta fitar daga Birnin New york na kasar Amurka. 

Taswirar yankin Kashmir, daya daga cikin yankunan da India da Pakistan ke takaddama akai
Taswirar yankin Kashmir, daya daga cikin yankunan da India da Pakistan ke takaddama akai
Talla

An cimma matsayar tsagaita wutan ne a yanki Kashmir bayan da aka samu sassantawa tsakani dakarun kasar India da na Pakistan.

Haka zalika matsayar na zuwa ne bayan da Khar ta yi kira zuwa ga hukumomin kasashen biyu da a tsagaita wuta a kan rikicin iyakokin kasashen biyu, al’amarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Hukumomin kasashen biyu na zargin juna da keta hakin bil adama sakamako kisa da aka yiwa wadansu soji biyu na kasar India, yayin da Firmanistan kasar India, Manmohan Singh, ya jaddada aniyar gwamnatin kasar India na gani cewar an daina zubda jinin tsakani kasashen biyu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.