Isa ga babban shafi
Pakistan

Harin bam ya kashe mutane 14 a Pakistan

Wani harin bam da aka kai a kasar Pakistan ya hallaka Sojin kasar 14 kana wasu 25 sun jikkata. Wannan harin dai ya auku ne a wani yanki mara isasshen tsaro dake kan iyakar kasar da kasar Afghanistan.  

Wani yanki da aka kai harin bam a kasar Pakistan
Wani yanki da aka kai harin bam a kasar Pakistan REUTERS/Naseer Ahmed
Talla

Wannan harin bam din an kai shi ne kan jerin gwanon motocin sojin kasar a kauyen Dosali na Arewacin Waziristan, wani wurin da ‘ya’yan kungiyar Taliban ke tsare dashi.

Jami’an tsaro ne dai suka bada tabbacin mutuwar Sojin 14, wasu 25 kuma rai a hannun Allah.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.